Leicester City F.C. | |
---|---|
| |
Bayanai | |
Suna a hukumance |
Leicester City Football Club |
Iri | ƙungiyar ƙwallon ƙafa |
Ƙasa | Birtaniya |
Laƙabi | The Foxes |
Mulki | |
Shugaba | Aiyawatt Srivaddhanaprabha (en) |
Hedkwata | Leicester |
Mamallaki | King Power (en) |
Mamallaki na |
Filbert Street (en) |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 1884 |
Awards received | |
|
Kungiyar Kwallon Kafa ta Leicester City ƙwararriyar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ce ta ƙasar Ingila wacce ke garin Leicester a Gabas ta Tsakiyar, Ingila. Kulob din na fafatawa a gasar Premier, matakin mafi girma a tsarin gasar kwallon kafa ta Ingila, kuma tana buga wasanninsa na gida a filin wasa na King Power Stadium.
An kafa kulob din a shekarar alif 1884 a matsayin Leicester Fosse FC, inda take wasa a filin kusa da Fosse Road. Sun koma Filbert Street a 1891, an zabe su zuwa Gasar Kwallon Kafa a 1894 kuma sun karɓi sunan Leicester City a 1919. Sun koma filin wasa na Walkers a shekara ta 2002, wanda aka sake masa suna zuwa King Power Stadium a 2011.